Dr. Alwan: "Yaren Ƙarfi" Shine Kawai Yaren Da Isra'ila Ke Fahimta

Shugaban Al-Wafa: Al'ummar Duniya, 'Yancin Ɗan Adam Ba Su Da Wani Amfani
26 Nuwamba 2025 - 19:45
Source: ABNA24
Dr. Alwan: "Yaren Ƙarfi" Shine Kawai Yaren Da Isra'ila Ke Fahimta

Gwamnatin mamayar Isra'ila ta sake aiwatar da kisan gilla kuma a sabon ta'addancinta, ta kashe "Haitham Ali Tabatabaei", ɗaya daga cikin fitattun kwamandojin Hizbullah na Lebanon.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Gwamnatin mamayar Isra'ila ta sake aiwatar da kisan gilla kuma a sabon ta'addancinta, ta kashe "Haitham Ali Tabatabaei", ɗaya daga cikin fitattun kwamandojin Hizbullah na Lebanon. Wannan kisan gilla wani ɓangare ne na manufofin siyasa da gwamnatin Sahyoniyawa ta tsara don kawar da shugabannin gwagwarmaya da gangan, wanda ya daɗe yana ci gaba da gudana tsawon shekaru.

Dr. Ahmed Alwan, shugaban Kungiyar Al-Wafa ta Lebanon kuma mai bincike kan batutuwan dabarun siyasa, ya bayyana a cikin wata hira da ABNA: Maƙiya Sahyoniyawa suna tunanin cewa ta hanyar kawar da kwamandoji, zasu iya gurgunta gwagwarmaya, amma Hizbullah ta dogara ne akan aikin haɗin gwiwa, tsarin mulki da kuma tsarin maye gurbin da aka tsara. Ga kowane kwamanda, akwai magada masu cikakken shiri da horo, kuma saboda wannan dalili, waɗannan kisan gillar ba wai kawai ba su raunana nufin gwagwarmayar ba, kai sai dai ma sun ƙarfafa ƙudurinta na ci gaba da kan wannan tafarki.

Babban Burin Gwamnatin Sahyoniyawa A Waɗannan Kisan Gillar

Wannan ƙwararren ɗan ƙasar Lebanon ya jaddada: Gwamnatin Sahyoniyawa tana son ta lalata shugabancin Lebanon da waɗannan kisan gilla da ta'addanci tare da yin kamar Lebanon ba ta bin alkawuran da ta ɗauka domin samun uzuri na ci gaba da mamaye ƙasar, rashin zaman lafiya, har ma da faɗaɗa aikin soja a Lebanon. A gaskiya ma, babban burin wannan gwamnatin shine cimma burin faɗaɗa ƙasar ta "Isra'ila Mafi Girma" da kuma wargaza gwagwarmaya da ke yankin gaba ɗaya.

Tasirin Kisan Gillar Akan Lissafin Kai Harin

Dr. Alwan ya jaddada cewa wannan kisan gillar ba zai haifar da wani cikas a cikin lissafin hana kai hari ba. An tsara tsarin gwagwarmaya ta yadda kowane shahidi zai sami magaji mai irin wannan matakin tsaro da ƙarfin soja. Ya ƙara da cewa: A duniyar yau, ra'ayoyi kamar "al'ummar ƙasa da ƙasa" da "haƙƙin ɗan adam" sun zama ba su da anfani, kuma hanyoyin shari'a na ƙasa da ƙasa sun gaza tabuka komai a ƙarƙashin mamayar Amurka da Sahyoniyawa; saboda haka, babu wani mai amsa kira da kawo tallafi ga mutanen Lebanon da ake zalunta.

Martanin Gwagwarmaya: Yaren Ƙarfi Da Fafatawa

Shugaban Kungiyar Al-Wafa ya ce: Tun bayan aiwatar da Kuduri na 1701 da yarjejeniyar tsagaita wuta, gwagwarmaya ce ta tabbata akan bin wannan yarjejeniya, yayin da gwamnatin Sahyoniyawa ta karya ta fiye da sau dubu biyar. Gwagwarmaya da ta fara gwada hanyar diflomasiyya, amma lokacin da bai yi aiki ba, ta dage martanin zuwa ga wani lokaci da hanyar da ta dace. Mafi kyawun yare don fuskantar gwamnatin Sahyoniyawa shine yaren ƙarfi, kuma Hizbullah da kanta za ta tantance lokaci, wuri, da ƙarfin martanin.

Wajibi Na Da Ya Hau Kan Gwamnatin Lebanon Da babban Haɗarin Kwance Ɗamarar Makamai 

Dr. Alwan ya ce: Gwamnatin Lebanon ba ta da ikon kare kanta da sojojin da ta ke da saboda iyakokin diflomasiyya da rashin kayan aikin soja na gaske (saboda iyakokin da Amurka ta sanya). Shirin kwance damarar makamai babban kuskure ne na dabarun siyasa. Madadin haka, gwamnati ya kamata ta matsa lamba sosai ga gwamnatin Isra'ila don ta janye gaba ɗaya daga yankin Lebanon, ta saki fursunoni, da kuma dakatar da kai hari. Shugaban Lebanon yana ƙoƙarin kare ƙasar daga yaƙi, amma gwamnatin Isra'ila ba ta neman zaman lafiya ba ne kawai.

Your Comment

You are replying to: .
captcha